Imam Baqir (AS) ya rawaito daga iyayensa: “Amirul Muminina (AS) ya yi huɗuba a ranar farko ta watan Azumi a masallacin Kufa. Sai ya yabi Allah da mafi kyawun yabo da mafi ɗaukakar yabo da isar da godiya, kuma ya aika da tsira ga Annabinsa Muhammad (SAW).”
Huɗubar Imam tana da bayani kamar haka:
“Ya ku mutane! Wannan wata, wata ne da Allah ya ɗaukaka shi a kan sauran watanni, kamar ɗaukakar mu Ahlul-Bait a kan sauran mutane. Kuma shi wata ne da ake buɗe ƙofofin sama da ƙofofin rahama a cikinsa, kuma ana rufe ƙofofin wuta a cikinsa. Kuma wata ne da ake jin kiran masu kira a cikinsa, kuma ana amsa addu’a, kuma ana tausayawa masu kuka.
Wata ne da a cikinsa akwai wani dare da mala’iku suke sauka daga sama, suna yi wa maza da mata masu azumi sallama da izinin Ubangijinsu har zuwa fitar alfijir, kuma wannan dare shi ne ‘Daren Lailatul Qadr’.
Shekaru dubu biyu kafin a halitta Adam (As), aka ƙaddara shugabancina (Wilaya) a cikin wannan dare. Yin azumi a cikinsa ya fi azumin watanni dubu alheri, kuma aiki a cikinsa ya fi aiki a cikin watanni dubu alheri.
Ya ku mutane! Ranar watan Ramadan tana haskawa a kan maza da mata masu azumi da rahama, kuma watansa yana haskaka su da rahama, kuma babu wani yini ko dare na wannan wata face Ubangiji Maɗaukaki yana zuba alheri a kan wannan al’umma.
Saboda haka, duk wanda ya amfana da kwayar zarra daga kwararar ni’imar Ubangiji, to a ranar saduwarsa da Allah, zai kasance mai daraja a gurin Allah, kuma babu wani bawa da zai kasance mai daraja a gurin Allah face Allah ya sanya Aljanna ta zama makomarsa.
bayin Allah! Wannan wata naku ba kamar sauran watanni yake ba. Ranakunsa su ne mafifitan ranaku, dararensa su ne mafifitan darare. Shi wata ne da ake ɗure shaiɗanu kuma ake ɗure su a kurkuku; watan da Allah Yake ƙara arziki da ajali a cikinsa, kuma Yake rubuta sunayen baƙin gidansa; watan da mutanen da suka yi imani ake karɓarsu da gafarar Ubangiji da yardarsa, da farin ciki da ni’imomin Ubangiji, da kuma yardar Sarki Mai Adalci da Iko.
Kai mai azumi! Ka duba da kyau cikin al’amarinka, domin a cikin wannan wata kai baƙon Ubangijinka ne. Ka duba yadda kake a cikin darenka da yininka, da yadda kake kiyaye gaɓobinka daga saɓon Allah.
Ka duba domin kada darenka ya kasance cikin barci kuma yininka cikin gafala; sai wannan wata ya shude maka alhalin nauyin zunubinka yana nan a wuyanka; sannan a lokacin da masu azumi suke karɓar ladansu, kai kuma ka kasance daga cikin masu nadama, kuma a lokacin da suke samun karamcin Sarkinsu, kai kuma ka kasance daga cikin waɗanda aka hana, kuma a lokacin da suke samun farin cikin makwabtaka da Ubangijinsu, kai kuma ka kasance daga cikin waɗanda aka kora!
Kai mai azumi! Idan aka kore ka daga ƙofar Majiɓincinka, wace ƙofa zaka fuskanta? Kuma idan Ubangijinka ya hana ka, wane ne zai ciyar da kai? Kuma idan ya wulakanta ka, wane ne zai girmama ka? Kuma idan ya kaskantar da kai, wane ne zai ba ka ɗaukaka? Kuma idan ya bar ka, wane ne zai taimake ka? Kuma idan bai karɓe ka ba a cikin taron bayinsa, ga wa zaka kai bautarka? Kuma idan bai yafe maka kuskurenka ba, ga wa zaka sa rai don gafarar zunubanka? Kuma idan ya nemi haƙƙinsa daga gare ka, me zai kasance hujjan ka?
Kai mai azumi! A cikin darenka da yininka ka kusanci Allah ta hanyar karatun littafin Allah, domin lallai littafin Allah mai ceto ne da ake karɓar cetonsa a ranar sakamako ga masu karatun Alkur’ani, kuma ta hanyar karanta ayoyinsa suna hauhawa cikin darajojin Aljanna.
al’bishir a gare ka kai mai azumi! Kana cikin watan da yin azuminka a cikinsa wajibi ne, numfashinka a cikinsa tasbihi ne, barcinka a cikinsa ibada ne, biyayyarka a cikinsa karɓabba ce, zunubanka a cikinsa gafartattu ne, sautukanka a cikinsa jiyayyu ne, kuma gudanar da dadadan kalamai na addu’a a cikinsa abin tausayawa ne. Na ji daga masoyina Manzon Allah yana cewa:
Ubangiji Maɗaukaki a lokacin buɗa baki na kowane dare na watan Ramadan, Yana da waɗanda Yake ‘yantarwa daga wuta, waɗanda babu wanda ya san adadinsu sai Allah. Adadinsu yana wurinsa a cikin ilimin gaibu. Saboda haka, idan daren ƙarshe na wannan wata ya karaso , Allah zai ‘yantar da misalin adadin duk mutanen da ya ‘yantar a duk tsawon wannan wata.
Wani mutum daga kabilar Hamdan ya tashi ya ce: Ya Amirul Muminina (amincin Allah ya tabbata a gare shi), ƙara mana bayani daga abin da masoyinka ya faɗa game da watan Ramadan.
Ya ce: To! Na ji ɗan’uwana kuma ɗan ammina, Manzon Allah, yana cewa: “Duk wanda ya yi azumin watan Ramadan kuma ya kiyaye kansa a cikin wannan wata daga abubuwan haram, zai shiga Aljanna.”
Wannan mutumin Hamdani ya ce: Ya Amirul Muminina (As), ƙara mana bayani daga abin da ɗan’uwanka kuma ɗan amminka ya faɗa game da watan Ramadan.
Ya ce: To! Na ji Manzon Allah yana cewa: “Duk wanda ya yi azumin watan Ramadan saboda imani da kuma neman ladan Ubangiji, zai shiga Aljanna.”
Mutumin Hamdani ya kara cewa: Ya Amirul Muminina (amincin Allah ya tabbata a gare shi), ƙara mana bayani daga abin da abokinka ya faɗa game da wannan wata.
Ya ce: To! Na ji shugaban na farko da na ƙarshe, Manzon Allah yana cewa: “Duk wanda ya yi azumin watan Ramadan kuma bai ci haram ba a dararensa, zai shiga Aljanna.”
Mutumin Hamdani ya kara cewa: Ya Amirul Muminina (amincin Allah ya tabbata a gare shi), ƙara mana bayani daga abin da shugaban na farko da na ƙarshe ya faɗa maka game da wannan wata.
Ya ce: To! Na ji mafificin Annabawa da Manzanni da Mala’iku makarrabai yana cewa: Lallai shugaban masu wasiyya za a kashe shi a cikin shugaban watanni. Na ce: Ya Manzon Allah! Wanne ne shugaban watanni, kuma wane ne shugaban masu wasiyya?
Ya ce: Amma shugaban watanni, shi ne watan Ramadan, kuma amma shugaban masu wasiyya, kai ne, ya Ali! Na ce: Ya Manzon Allah, shin hakan zai kasance? Ya ce: Ƙwarai kuwa, na rantse da Ubangijina! Lallai mafi lallacewar al’ummar ta, ɗan’uwan wanda ya soki raƙumar Samud, zai tashi ya buge ka a tsakiyar kanka, wanda gashin bakinka da gemunka zai rine da jininsa.
Sai mutane suka shiga kuka da ruri. Kuma halar Amirul Muminina Ali (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kammala huɗubarsa kuma ya sauko.
Madatta
Fada’il al-Ashhur al-Thalathah, Sheikh Saduq, shafi na 108
Kitab Mah-e Khoda, juzu’i na 1, shafi na 176.