Most searched:

Ziyarar Arba’in

Sheikh Dabari a cikin littattafanta "Tahdzib" da "Misbah" ya rawaito daga Imam Hasan al-Askari (A.S.) cewa alamomin mu'mini guda biyar ne: Karanta rakaa hamsin da daya wacce nufinta yake shi ne rakaa goma sha bakwai na wajibi da rakaa talatin da hudu na nafila a kowane dare da rana, da ziyarar Arba'in, da sa zobe a hannun dama, da a doron kasa sanya goshi a lokacin sujada, da furta babbar murya: "Bismillaahir-Rahmaanir-Rahīm". Yadda ake ziyarar Imam Husseini (A.S.) a ranar Arba'in ta zo a haka:

Arba’in din Sayyidush-Shuhadaa (A.S.) ta yi daidai da rana ta ashirin ta watan Safar; Ziyarar Arba’in ziyara ce wacce Sheikh a cikin littattafansa biyu “Misbah” da “Tahdzib” ya rawaito daga Safwan Jammaal cewa Safwan ya ce: Uban-gidana Imam Sadiq (A.S.) ya gaya mani game da ziyarar Arba’in: Lokacin faduwar rana, ka karanta:

السَّلامُ عَلَی وَلِی اللّهِ وَحَبِیبِهِ، السَّلامُ عَلَی خَلِیلِ اللّهِ وَنَجِیبِهِ، السَّلامُ عَلَی صَفِی اللّهِ وَابْنِ صَفِیهِ، السَّلامُ عَلَی الْحُسَینِ الْمَظْلُومِ الشَّهِیدِ، السَّلامُ عَلَی أَسِیرِ الْکرُباتِ وَقَتِیلِ الْعَبَرَات.

اللّهُمَّ إِنِّی أَشْهَدُ أَنَّهُ وَ لِیک وَابْنُ وَلِیک، وَصَفِیک وَابْنُ صَفِیک، الْفَائِزُ بِکرَامَتِک، أَکرَمْتَهُ بِالشَّهَادَةِ، وَحَبَوْتَهُ بِالسَّعَادَةِ، وَاجْتَبَیتَهُ بِطِیبِ الْوِلادَةِ، وَجَعَلْتَهُ سَیداً مِنَ السَّادَةِ، وَقَائِداً مِنَ الْقَادَةِ، وَذَائِداً مِنَ الذَّادَةِ، وَأَعْطَیتَهُ مَوَارِیثَ الْأَنْبِیاءِ، وَجَعَلْتَهُ حُجَّةً عَلَی خَلْقِک مِنَ الْأَوْصِیاءِ، فَأَعْذَرَ فِی الدُّعَاءِ، وَمَنَحَ النُّصْحَ،

وَبَذَلَ مُهْجَتَهُ فِیک لِیسْتَنْقِذَ عِبَادَک مِنَ الْجَهَالَةِ، وَحَیرَةِ الضَّلالَةِ، وَقَدْ تَوَازَرَ عَلَیهِ مَنْ غَرَّتْهُ الدُّنْیا، وَبَاعَ حَظَّهُ بِالْأَرْذَلِ الْأَدْنی، وَشَرَی آخِرَتَهُ بِالثَّمَنِ الْأَوْکسِ، وَتَغَطْرَسَ وَتَرَدَّی فِی هَوَاهُ، وَأَسْخَطَک وَأَسْخَطَ نَبِیک وَأَطَاعَ مِنْ عِبادِک أَهْلَ الشِّقاقِ وَالنِّفاقِ، وَحَمَلَةَ الْأَوْزارِ، الْمُسْتَوْجِبِینَ النَّارَ، فَجاهَدَهُمْ فِیک صابِراً مُحْتَسِباً حَتَّی سُفِک فِی طَاعَتِک دَمُهُ وَاسْتُبِیحَ حَرِیمُهُ؛ اللّهُمَّ فَالْعَنْهُمْ لَعْناً وَبِیلاً، وَعَذِّبْهُمْ عَذاباً أَلِیماً.

السَّلامُ عَلَیک یا ابْنَ رَسُولِ اللّهِ، السَّلامُ عَلَیک یا ابْنَ سَیدِ الْأَوْصِیاءِ، أَشْهَدُ أَنَّک أَمِینُ اللّهِ وَابْنُ أَمِینِهِ، عِشْتَ سَعِیداً، وَمَضَیتَ حَمِیداً، وَمُتَّ فَقِیداً، مَظْلُوماً شَهِیداً، وَأَشْهَدُ أَنَّ اللّهَ مُنْجِزٌ مَا وَعَدَک، وَمُهْلِک مَنْ خَذَلَک، وَمُعَذِّبٌ مَنْ قَتَلَک، وَأَشْهَدُ أَنَّک وَفَیتَ بِعَهْدِ اللّهِ، وَجاهَدْتَ فِی سَبِیلِهِ حَتّی أَتَاک الْیقِینُ، فَلَعَنَ اللّهُ مَنْ قَتَلَک، وَلَعَنَ اللّهُ مَنْ ظَلَمَک، وَلَعَنَ اللّهُ أُمَّةً سَمِعَتْ بِذلِک فَرَضِیتْ بِهِ؛

اللّهُمَّ إِنِّی أُشْهِدُک أَنِّی وَلِی لِمَنْ والاهُ، وَعَدُوٌّ لِمَنْ عاداهُ، بِأَبِی أَنْتَ وَأُمِّی یا ابْنَ رَسُولِ اللّهِ، أَشْهَدُ أَنَّک کنْتَ نُوراً فِی الْأَصْلابِ الشَّامِخَةِ، وَالْأَرْحامِ الْمُطَهَّرَةِ، لَمْ تُنَجِّسْک الْجاهِلِیةُ بِأَنْجاسِها، وَلَمْ تُلْبِسْک الْمُدْلَهِمَّاتُ مِنْ ثِیابِها، وَأَشْهَدُ أَنَّک مِنْ دَعائِمِ الدِّینِ، وَأَرْکانِ الْمُسْلِمِینَ، وَمَعْقِلِ الْمُؤْمِنِینَ، وَأَشْهَدُ أَنَّک الْإِمامُ الْبَرُّ التَّقِی الرَّضِی الزَّکی الْهادِی الْمَهْدِی،

وَأَشْهَدُ أَنَّ الْأَئِمَّةَ مِنْ وُلْدِک کلِمَةُ التَّقْوی، وَأَعْلامُ الْهُدی، وَالْعُرْوَةُ الْوُثْقی، وَالْحُجَّةُ عَلَی أَهْلِ الدُّنْیا، وَأَشْهَدُ أَنِّی بِکمْ مُؤْمِنٌ، وَبِإِیابِکمْ مُوقِنٌ، بِشَرایعِ دِینِی، وَخَواتِیمِ عَمَلِی، وَقَلْبِی لِقَلْبِکمْ سِلْمٌ، وَأَمْرِی لِأَمْرِکمْ مُتَّبِعٌ، وَنُصْرَتِی لَکمْ مُعَدَّةٌ حَتَّی یأْذَنَ اللّهُ لَکمْ، فَمَعَکمْ مَعَکمْ لَامَعَ عَدُّوِکمْ، صَلَواتُ اللّهِ عَلَیکمْ، وَعَلَی أَرْواحِکمْ وَأَجْسادِکمْ، وَشاهِدِکمْ وَغَائِبِکمْ، وَظَاهِرِکمْ وَبَاطِنِکمْ، آمِینَ رَبَّ الْعالَمِینَ.

Amincin Allah ta tabbata ga Waliyin Allah da masoyinshi, Amincin Allah ya tabbata  ga Masoyin Allah kuma fitacce kuma madaukakinshi, Amincin Allah ya tabbata ga bawan Allah zaɓaɓɓen da ɗanshi zababbe, Amincin Allah ya tabbata ga Husseini wanda aka zalunta kuma shahidi, Amincin Allah ya tabbata ga wanda ya fuskanci damuwa da wanda aka kashe shi da hawaye,

Ya Allah ina shaida cewa Husseini Waliyi ne naka kuma dan Waliyi, kuma zababben ka kuma dan zaɓaɓɓen ka,  wanda ya kai ga karimcin Ka kuma Ka girmama shi da shahada kuma Ka kebanta shi da farin cikinsa kuma Ka zabe shi da tsaftar haihuwa kuma Ka sanya shi shugaba daga cikin shugabanni da jagora daga cikin jagorori da mai kare hakki daga cikin masu kare hakki kuma Ka ba shi gado na annabawa kuma Ka sanya shi hujja a kan bayinka daga cikin halifofi, kuma a kiran da ya yi bai bar wani uzuri ba kuma bai nuna rowa ba a cikin shawarar kirki,

Kuma ya sadaukar da ransa a cikin hanyar Ka domin ya ceton bayinka daga jahilci da yawon bace-bace, a yayin da suka hada kai domin yaki da shi wadanda duniya ta yaudare su kuma suka sayar da rabonsu na gaskiya ga abin da ya fi kaskanci kuma suka sayar da lahirarsu ga mafi karancin farashi a kasuwar sayarwa, suka yi girman kai suka sanya kansu a cikin sha’awar rai, suka fusatar da Kai da Manzon Ka kuma suka bi daga cikin bayinka mutanen rarraba da munafunci da masu daukar manyan zunubai da masu cancantar wuta, sai ya yi yaki da su saboda Kai da hakuri kuma saboda Kai yayi jihadi har aka zubar da jininsa a cikin biyayyar Ka kuma aka halatta haraminsa; Ya Allah Ka la’anci su la’anta mai nauyi kuma Ka azabtar da su azaba mai zafi,

Amincin Allah ya tabbata a gare ka Ya dan Manzon Allah, Amincin Allah ya tabbata a gare ka Ya dan shugaban halifofi, ina shaida cewa kai amintaccen Allah ne kuma dan amintaccensa ne, kayi rayuwa cikin farin ciki kuma ka mutu kana mai yabo kuma ka bar duniya kana mai daga cikin wanda aka zalunta da shahidi, ina shaida cewa Allah mai cika alkawari ne abin da Yayi maka alkawari da shi kuma mai halakar da wadanda suka yi rowa wajen taimakonka da mai azabtar da wadanda suka kashe ka kuma ina shaida cewa ka cika alkawarin Allah kuma ka tashi da jihadi a hanyar Sa har mutuwa ta zo maka, Allah Ya la’anci wadanda suka kashe ka suka zalunce ka kuma suka ji wannan labari suka yi farin ciki da shi;

Ya Allah ina sanya Ka shaida cewa ni aboki ne ga wanda yake son shi kuma makiyi ne ga wanda yake gaba da shi, uba na da uwata su zama fansa a gare ka Ya dan Manzon Allah, ina shaida cewa ka kasance a cikin kashin bayana madaukaka da mahaifa masu tsafta, jahiliyya ba ta bata ka ba da kazantarta ba kuma bata taba tufafinta masu duhu da bakake, kuma ina shaida cewa kai ka kasance ginshikan addini da asalin Musulmai da mafakar mutane mu’minai kuma ina shaida cewa kai shugaba ne mai kyau, mai tsoron Allah, mai yarda da kaddarorin gaskiya, mai tsarki, mai shiryarwa kuma wanda aka shiryar.

Kuma ina shaida cewa Imamai daga zuriyarka su ne asalin tsoron Allah da alamomin shirya da igiya mika da hujja a kan mutanen duniya, kuma ina shaida cewa ni hakika mai imani ne gare ku kuma ina da tabbatacce kan komawar ku, a bisa dokokin addinina da karshen ayyukana kuma zuciyata tana tare da zuciyarku cikin amincewa kuma aikina yana bin aikin ku kuma taimakona a shirye yake a gare ku har sai Allah Ya ba ku izini, sai ina tare da ku ba tare da makiyan ku ba, tsarkin Allah ya tabbata a gare ku da ruhokinku da jikunanku da wanda yake a nan da wanda yake boye da bayyananne naku, Amin Ya Ubangijin talikai.

Sa’annan kayi rakaa biyu ka roki abin da kake so.

Ƙarin abubuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *