- Umar bin Yahya al-Alawi ya gina sabon babban daki (harami) tare da wata doguwar kubba ta musamman. Wannan mutum yana da wata babbar daraja; wato maida bakin dutse (Hajarul Aswad) daga hannun kungiyar Qaramita wadanda mabiya darikar Isma’iliyya ne, inda ya maida shi mazauninsa na asali a cikin dakin Ka’aba mai alfarma.
Maida Hajarul Aswad da Sabon Ginin Harami Sayyid Ja’afar Bahrul Ulum ya rubuta game da wannan ginin cewa: «Wannan ginin an yi shi ne ta hannun Sayyid Abul-Ula Umar, babban mutum wanda Allah ya sanya aka dawo da Hajarul Aswad ta hannunsa, bayan da kungiyar Isma’iliyya ta kai hari Makka a shekara ta 317 bayan hijira, suka kwashe ganimar Hajarul Aswad zuwa Kufa suka rataye shi a kan shika-shiki na bakwai na masallacin Kufa.
Labarin yana da tsawo. Shi wannan babban mutum (Sayyid) ya mayar da dutsen (Hajarul Aswad) mazauninsa na asali a shekara ta 339 bayan hijira, bayan ta shafe shekaru 22 a hannunsu.
Wannan mutum mai daraja ya gina kubbar kakansa Amirul Muminina (A.S) da dukiyar kansa. Shi jikan Husain Zi-Dam’ah ne, kuma tsarinsa na nasaba shi ne: Abul-Ula Umar bin Yahya, gwamnan Kufa, dan Husain Naqib Tahir, dan Abu Atiqa Ahmad (mawaƙi kuma masanin hadisi), dan Abul-Ula Umar bin Abal-Husain Yahya, daya daga cikin sahabban Imam Kazim (A.S) wanda ya yi shahada a shekara ta 250 bayan hijira.»
Sheikh Muhammad Husain Hirzuddin ya fadi game da Naqibul Talibiyyin, Sayyid Umar al-Alawi cewa: «Allah ya karrama shi da wasu siffofi guda biyu fitattu: Na farko, gina kubbar kakansa mai girma, Amirul Muminina (A.S) da dukiyar kansa. Na biyu kuma shi ne maida Hajarul Aswad zuwa mazauninta na asali.
A shekara ta 339 bayan hijira, Sayyid Abul-Ula Umar bin Yahya al-Alawi ya shiga tsakani tsakanin halifa al-Muti’ Lillah da kungiyar Isma’iliyya, inda ya samu nasarar dawo da Hajarul Aswad.
Da farko an kawo ta Kufa aka rataye ta a shika-shiki na bakwai na masallaci kafin daga bisani a kai ta dakin Allah. Wannan lamari ya tabbatar da wata riwaya da aka samo daga Amirul Muminina (A.S) inda ya fada cewa: Za a sace Hajarul Aswad kuma a rataye ta a kan shika-shiki na bakwai.»
Madogarar Bayani:
An ciro daga littafin «Tarihin Haikali Mai Alfarma na Alawi» (Tarikh al-Marqad al-Alawi al-Mutahhar).