Ginin fasali na biyu na kabarin Amirul Muminina (A.S) an gina shi ne bisa umarnin gwamnan Mosul, Amir Abul-Haija Abdullah bin Hamdan al-Hamdani, a cikin shekaru goma na farkon karni na hudu bayan hijira, a lokacin halifancin al-Muqtadir Billah al-Abbasi (295-317 bayan hijira).
Dokta Salah Fartusi ya yi hasashen cewa an gina wannan ginin ne a shekara ta 311 bayan hijira, inda yake rubutawa cewa:
«Babu wani mai bincike da ya yi nasarar gano takamaiman ranar gina wannan ginin, amma a ra’ayina, an bayar da umarnin gina shi ne a shekara ta 311 bayan hijira. Domin kuwa a wannan shekarar ne aka nada Abul-Haija a matsayin wakilin halifa don jagorancin aikin hajji.
Wataƙila ya tsaya a Kufa yayin tafiyarsa – kamar yadda mahajjata daga Iraki suka saba yi – inda ya ziyarci kabari mai alfarma na Amirul Muminina (A.S), ya ba da umarnin gina ginin, sannan ya wuce don gudanar da aikin hajji.»
Kubba mai Kusurwa Hudu
Ibn Hauqal (wanda ya rasu a shekara ta 380 bayan hijira) shi ma ya rubuta cewa:
«Abul-Haija Abdullah bin Hamdan ya bayyana wannan wuri ga mutane, kuma ya gina katanga mai karfi a kewaye da shi. Ya gina wata katuwar kubba mai tsawo a kan kabarin wadda take da kusurwa hudu da kofofi da dama, sannan ya lullube ta da labule masu daraja, ya kuma shimfida mata mafi kyawun kafet. A wannan wurin, an binne da yawa daga cikin ‘ya’yansa da manyan zuriyar gidan Abu Talib a wajen wannan kubbar, kuma filin da ke kewayen katangar ya zama makabartar zuriyar Abu Talib.»
Wannan katangar ita ce bangon farko da ya kewaye gidajen sabon birnin da ya kafu a kewayen kabarin Amirul Muminina (A.S); kamar yadda munduwa take kewaye da wuyan hannu. Binciken matanin tarihi ya nuna cewa ana binne matattu ne a cikin birnin da kuma kusa da bangayensa.
Al-Idrisi (wanda ya rasu a shekara ta 559 bayan hijira) ya rubuta cewa:
«A tazarar kilomita shida daga Kufa, ana iya ganin wata doguwar kubba mai kyan gaske wadda take da kusurwa hudu. Wannan kubba tana da kofofi a kowane bangare wadanda suke a kulle kuma aka lullube su da labule masu kyau da daraja. An shimfida mata kafet masu inganci. Ana cewa kabarin Ali bin Abi Talib yana cikinta, kuma kewayen kubbar makabarta ce ta zuriyar gidan Abu Talib. Wannan kubbar Abul-Haija Abdullah bin Hamdan ne ya gina ta a zamanin Abbasiyawa, bayan ta kasance a boye a zamanin Umayyawa.»
Ibnul Wardi (wanda ya rasu a shekara ta 852 ko 861 bayan hijira) ya rubuta game da Kufa cewa:
«Akwai wata katuwar kubba a Kufa wadda ake cewa kabarin Ali bin Abi Talib ne a cikinta, kuma kewayen kubbar makabarta ce ta zuriyar gidan Ali. An gina wannan kubbar ne bisa umarnin Abul-Abbas Abdullah bin Hamdan a zamanin Abbasiyawa.»
Sheikh Ja’afar Mahbuba shi ma ya nakalto daga rubutun hannu na Sheikh Ali Al Kashiful Ghita mai taken «Samirul Hadir wa Anisul Musafir» cewa:
«Zuriyar Hamdan (Al Hamdan) suna kwaso gawarwakin matattunsu daga Sham, Aleppo (Halab), Diyarbakir, Mosul, Farisa (Fars), da Iraki zuwa Najaf, kuma suna kawo kyaututtuka masu daraja zuwa kabarin Amirul Muminina (A.S), wadanda suka hada da fitilun zinariya da azurfa, takubba masu ado da duwatsu masu daraja, da sauran kayayyaki masu kima daga sarakuna, maza, mata, da ‘ya’yansu, wadanda a lokacin rubuta wannan littafi suna nan a taskar hubbaren Alawi (al-Khizanah al-Gharawiyyah).»
Madogarar Bayani:
An ciro daga littafin «Tarihin Haikali Mai Alfarma na Alawi» (Tarikh al-Marqad al-Alawi al-Mutahhar).