Atabatul Alawiyya Mai Tsarki ta yi kyakkyawar tarba ga iyalan shahidai na makarantar “Shajareh Tayyibaeh” a birnin Minab, da ke kudancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. An gudanar da wannan mataki a matsayin wani shirin jin kai wanda ke da nufin karbar bakuncin iyalan shahidai da wadanda suka rasa ‘ya’yansu a yakin kwanan nan, tare da samar musu da damar ziyartar Haramin Amirul Muminin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) mai tsarki da Ataba masu tsarki na Iraki.
Haidar Al-Isawi, shugaban kwamitin ayarin bayar da dauki kuma memba a kwamitin gudanarwa na Atabatul Alawiyya Mai Tsarki, yayin da yake halartar taron tare da iyalan da aka yi wa juyayi, ya bayyana wa Cibiyar Labarai ta Ataba cewa: “Atabatul Alawiyya Mai Tsarki ta fara wannan matakin jin kai ne don karbar bakuncin iyalan dalibai da ma’aikatan ilimi na makarantar ‘Shajareh Tayyibeh’ a birnin Minab wadanda suka rasa rayukansu a harin wuce gona da iri na Amurka da sahyoniyawa.”
Ya kara da cewa: “Wannan ayari shi ne kashi na farko na wani cikakken shiri da ake aiwatarwa da nufin bayar da tallafi da kasancewa tare da iyalan shahidai da suka yi shahada a yakin kwanan nan, da rage radadin bakin ciki da sakamakon wannan musiba. Wannan shiri ya kunshi ziyartar Haramin Amirul Muminin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) mai tsarki, Maziya masu tsarki na Najaf al-Ashraf, da kuma Ataba masu tsarki na Karbala, Kazimiyya, da Samarra, baya ga gudanar da bukukuwan karramawa na musamman ga iyalan.”
Godiya ga Hadin Kai da Juyayi
Mahaifin shahida Zainab Makki-Zadeh ya ce: “Ziyarar Najaf al-Ashraf ga iyalan shahidai, wani wuri ne na samun nutsuwa da juyayi.”
Ya nuna godiyarsa ga Atabatul Alawiyya Mai Tsarki, al’ummar Iraki, da mazaunan Najaf al-Ashraf bisa kyakkyawar tarba, karimci, da kulawar jin kai da suka nuna, ya kuma ce wadannan dabi’u sun dan rage nauyin radadin rashin da bakin cikin iyalan.
Raunin da Ba a Iya Kwatanta Shi
Mahaifin shahidi Arsha Mirani shi ma ya yi jawabi mai tsuma zuciya game da girman musibar da iyalan suka fuskanta, yana mai cewa: “Rasa ‘ya’ya wani rauni ne da ba a iya kwatanta shi da kowace kalma, kuma fuskantar gawarwakin yara bayan harin ya wuce karfin juriyar kowane uba da uwa.”
Ya kara da cewa: “Alamun barnar da suka rage a wurin da abin ya faru har yanzu shaida ce ta girman wannan musiba; amma kulawa, taimako, da kaunar da iyalan suka gani a lokacin wannan tafiya, ya dan rage radadinsu da wahalarsu sannan ya ba su jin hadin kai da tallafi.”
Har ila yau ya jaddada cewa Atabatul Alawiyya Mai Tsarki ta samar da dukkanin bukatu na wannan tafiyar ziyara, gami da sufuri, masauki, tarba, da shirye-shirye na musamman, sannan ya yaba da tsari da himmar mahukunta wajen aiwatar da wannan shiri. Haka nan ya yaba da yadda al’ummar Najaf al-Ashraf suka nuna kauna da juyayi ga iyalan shahidai.
Na Kasa Yin Sallama Da ‘Dana
A wani bayanin, mahaifin shahidi Subhan Shahdadi ya tuna da lokutan karshe inda ya ce: “Ban samu damar yin sallama da ‘dana kamar yadda sauran iyaye suka yi ba; domin na kasance ina tsaye a gaban gawarsa kuma ba ni da karfin fahimtar wannan musiba. Hoton ‘dana da abubuwan da na tuna da shi har yanzu suna raye a raina kuma ba zan taba mantawa da su ba.”
Ya kamata a lura cewa harin makami mai linzami da Amurka ta kai a wannan makaranta a lokacin sa’o’in aiki a hukumance, ya haifar da shahadar dalibai 168 da malamai 25; mutanen da suke gudanar da ayyukansu na koyarwa da na jin kai.
An aiwatar da wannan matakin jin kai ne a cikin tsarin kokarin Atabatul Alawiyya Mai Tsarki na nuna juyayi ga iyalan shahidai, bayar da tallafi a gare su, da kuma bayyana al’adar hadin kai ta jin kai da aka jaddada a cikin tarihin rayuwar Amirul Muminin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).




