Kwamitin tallafawa Maukibobin Imam Husseini, ya fara raba abubuwan bukata tsakanin Maukibobin da ke bayar da hidima ga wadanda suke shiga cikin taron Arba’in na Imam Husseini.
A cikin wannan shiri, ana raba fakitin kayan abinci da ruwan sha tsakanin Maukibobin da ke cikin tsohon garin Najaf da kuma yankunan da ke kusa da haramin Amiral Muminina Imam Ali (Aminci ya tabbata a gare shi) don karfafar masu yiwa miliyoyin maziyartan Arba’in hidima a Najaf al-Ashraf.
Ahmad Najm al-Rikabi, shugaban kwamitin tallafawa Maukibobin Imam Husseini, ya bayyana game da hakan cewa: “Kwamitin ya fara gudanar da tsarin raba kayan abinci tsakanin Maukibobin Imam Husseini fiye da 1500. Wadannan Maukibobin suna kan hanyoyin da suka tunkari tsohon garin da kuma kewayen haramin Amiral Muminina Imam Ali (Aminci ya tabbata a gare shi).”
Ya kara da cewa: “Kason da aka ware wa kowane maukibi ya kunshi shinkafa, mai, tumatur na gwangwani da kuma wasu kayan abinci daban-daban. Haka nan kuma ana samar da ruwan sha gwargwadon bukata don kara musu karfin bayar da mafi kyawun hidima ga maziyarta a kwanakin wannan ziyara ta miliyoyin mutane.”
Kwamitin tallafawa Maukibobin Imam Husseini bisa ga wani shiri na fili, yana gudanar da tsarin raba abubuwan bukata ta yadda dukkan Maukibobin da abin ya shafa za su amfana da wannan tallafi; wani mataki da ake aiwatarwa don karfafa ayyukan sa kai, bayar da hidima da kuma taimakawa wajen gudanar da taron Arba’in na Imam Husseini cikin nasara da daukaka.









