Most searched:

Mika tuta mai albarka ta Imam Hassan (Aminci ya tabbata a gare shi) ga Atabutul Alawiyya

Atabutul Abbasiyya, ta mika tuta mai albarka ta Imam Hassan Al-Mujtaba (Aminci ya tabbata a gare shi) ga Atabutul Alawiyya a kan munasabar zagayowar ranar shahadarsa.

Atabutul Alawiyya, ta kasance mai masaukin baki ga wata tawaga daga Atabutul Abbasiyya karkashin jagorancin “Sayyid Lais Al-Musawi” mamba a kwamitin gudanarwa, tare da wasu daga cikin ma’aikatan sashen lamuran addini da na hulda da jama’a na wannan harami.

An tarbi wannan tawaga ne daga wajen “Wissam Al-Haddad” mamba a kwamitin gudanarwa na Atabutul Alawiyya da kuma wasu daga cikin wakilan sashen hulda da jama’a.

A yayin wannan ganawa, an mika tuta mai albarka ta Imam Hassan Al-Mujtaba (Aminci ya tabbata a gare shi) ga Atabutul Alawiyya.

An gudanar da wannan mataki ne don girmama zagayowar ranar shahadarsa, wanda yayi daidai da ranar bakwai ga watan Safar, kuma an gudanar da shi a cikin wani yanayi cike da aminci da kyakkyawar alaka ta ruhi tsakanin haramomi masu tsarki guda biyu.

Ƙarin abubuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *