Sashen masaukin maziyarta na Atabutul Alawiyya Mai Tsarki, tun daga ranar bakwai ga watan Safar a kan turbar shirye-shiryen da wuri domin bayar da hidima ga maziyartan Arba’in, ya fara raba abinci mai albarka a tsakanin maziyartan Arba’in na Aba Abdillah Imam Husseini (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wadanda suke samun girmamawar ziyartar Harami mai tsarki na shugaban masu tsoron Allah sannan su nufi garin Karbala mai alfarma.
Asir Al-Tamimi, shugaban sashen masaukin maziyarta na Atabutul Alawiyya Mai Tsarki, a wata hira da Cibiyar Labarai ta Ataba ya bayyana cewa: “A daidai lokacin isowar miliyoyin maziyarta da wuri Haramin Amiral Muminina (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) mai tsarki, an fara karbar bakuncinsu ta babbar kofar shiga babban ginin masaukin maziyarta, wanda ke kusa da harabar Sayyada Fadima (Amincin Allah ya tabbata a gare ta).
Haka nan kuma, a daidai lokacin ranar tunawa da shahadar mai karamcin Ahlul Baiti, wato Imam Hassan (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), an tanadi wani buki na karamcin Alawi domin maziyarta.”
Ya kara da cewa: “Bisa umarnin Jagorancin Atabutul Alawiyya Mai Tsarki, da yawa daga cikin cibiyoyin bayar da hidima, karbar baki da wuraren hutawar maziyartan Arba’in sun fara gudanar da ayyukansu tun a kwanakin farko-farko.
Wadannan cibiyoyi sun kunshi tashoshi da ke kewayen haraba mai tsarki ta Haidari, wurare a kan hanyoyin da suka nufi Haramin Amiral Muminina (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a cikin tsohon tsarin garin Najaf al-Ashraf gami da tashoshin karbar baki a kan hanyar tattakin Arba’in; hanyar da miliyoyin maziyarta a kan hanyarsu ta zuwa garin Karbala mai alfarma suke wucewa daga garin Najaf al-Ashraf.”
Yana da kyau a lura cewa Atabutul Alawiyya Mai Tsarki, ta hanyar amfani da dukkanin karfinta da sassanta, tana shiga cikin bayar da hidima ga maziyartan Arba’in na Aba Abdillah Imam Husseini (Amincin Allah ya tabbata a gare shi); maziyartan da suke zaben Haramin Amiral Muminina (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) mai tsarki a garin Najaf al-Ashraf a matsayin daya daga cikin manyan tashoshin hanyarsu zuwa garin Karbala mai alfarma domin yin tattakin Arba’in.




