Yaƙin Siffin ba yaƙin soja kaɗai ba ne, bari ma ya kasance wani muhimmin wani abu da ya kowo sauyi a tarihin Musulunci. Mu’awiya, wanda yake mulki a Sham, ya ƙi yin mubaya’a ga Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), kuma ya kafa runduna domin yaƙi da Imam da hujjar ɗaukar fansar jinin Usman.
A ɗaya ɓangaren kuma, wannan yaƙi ya ƙarfafa matsayin Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a matsayin shugaba mai adalci kuma mai kare gaskiya, ya kuma bayyana rawar da ya taka wajen kiyaye haɗin kan Musulmi.
Kira zuwa Mubaya’a
Domin hana yaƙi da zubar da jini, Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yanke shawarar aika wa Mu’awiya wasiƙa yana kiransa zuwa mubaya’a da biyayya. Jarir ɗan Abdullah, ɗaya daga cikin shahararrun Sahabbai, ya kai wasiƙar zuwa Sham.
Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya rubuta wa Jarir:
“Bayan wasiƙata ta isa gare ka, ka tilasta wa Mu’awiya ya zaɓi ɗaya daga cikin hanyoyi biyu: ‘yaƙi mai kawo wulakanci’ ko ‘sulhu mai kawo yardar rai.’ Idan ya zaɓi yaƙi, ka sanar da shi cewa na barranta daga gare shi; idan kuma ya zaɓi sulhu, ka karɓi mubaya’arsa.”
Da wasiƙar ta isa hannun Jarir, ya kai ta wajen Mu’awiya ya karanta masa. Sannan ya ce:
“Ya Mu’awiya! Ba a rufe zuciya sai saboda zunubi, kuma ba a buɗe ta sai da tuba. Ina zaton an rufe zuciyarka da zunubi. Ina ganinka tsaye tsakanin gaskiya da ɓata, kamar kana jiran abin da wasu za su yi.”
Mu’awiya ya amsa:
“Da izinin Allah, zan ba ka cikakkiyar amsa a farkon damar da na samu.” [1]
Martanin Mu’awiya da Amsar Jagoran Masu Taqawa
Jarir ɗan Abdullah ya kai wa Mu’awiya wasiƙar Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), amma maimakon ya karɓi kiran mubaya’a, Mu’awiya ya ƙi yin biyayya ga Jagoran Masu Taqawa, yana mai fakewa da hujjar ɗaukar fansar jinin Usman.
A martaninsa ga wasiƙar Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), Mu’awiya ya ce wa Jarir:
“Ka rubuta wa shugabanka, Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ka roƙe shi ya ba ni Sham da Masar tare da harajinsu. Haka kuma, ya tabbatar da cewa bayan mutuwarsa ba wata mubaya’a za ta rataya a wuyana ba. A lokacin ne zan yi masa mubaya’a kuma in amince da halifancinsa.”
Jarir ya ce:
“Ka rubuta duk abin da kake so, ni ma zan rubuta tare da kai.”
Sai Mu’awiya ya rubuta wa Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).
Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya rubuta wa Jarir a matsayin martani:
“Mu’awiya yana son kada wata mubaya’a ta rataya a wuyansa, kuma kada ya bi umarnina. Haka kuma yana son ya yaudare ka domin ya jawo mutanen Sham zuwa ɓangarensa. Mughira ɗan Shu’ba ya ba ni shawara a Madina cewa in naɗa Mu’awiya a matsayin gwamnan Sham, amma ban amince ba, domin Allah ba Ya son Ya ganni ina taimakon masu ɓatarwa. Idan Mu’awiya yayi mubaya’a, to alheri; idan kuma bai yi ba, ka dawo.”
Wasiƙar Mu’awiya ta bazu a tsakanin Larabawa. [2]
Cikakkiyar Amsa ga Da’awar Mu’awiya
Lokacin da Mu’awiya ya karɓi mubaya’a daga mutanen Sham, ya rubuta wasiƙar kiran yaƙi, sannan ya ce wa Jarir, manzon Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi):
“Ka koma wajen abokin tafiyarka, Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).”
Sai Amirul Muuminiin ya rubuta a martani:
“Daga Ali zuwa ga Mu’awiya ɗan Sakhr. Wasiƙa ta iso gare ni daga mutumin da ba shi da basira da za ta shiryar da shi, kuma ba shi da shugaba da zai nuna masa hanya. Son zuciya ne ya kira shi, shi kuma ya amsa kiran ransa; sai ɓata ta kama ragamarsa, ya bi ta.
Ka yi zaton cewa ambaton kuskurena game da Usman ya lalata mubaya’ata a kanka. Wallahi, ni ɗaya ne kawai daga cikin Muhajirai. Kamar yadda suka shiga Musulunci, nima na shiga; kamar yadda suka tashi tsaye domin Musulunci, nima na tashi. Allah ba Zai tara su a kan ɓata ba, kuma ba Zai makantar da zukatansu ba. Ban ba da umarnin kashe shi ba har laifin mutuwarsa ya rataya a wuyana, kuma ban kashe shi ba har na cancanci a nemi fansa daga gare ni.
Game da maganarka cewa: ‘Yanzu mutanen Sham ne suke da iko a kan mutanen Hijaz,’ ka nuna mini wani mutum daga Quraishawan Sham wanda za a amince da shi a majalisar shawara, ko wanda ya cancanci halifanci. Idan ka yi wannan da’awar, Muhajirai da Ansar za su ƙaryata ka, sai dai idan ka nuna wani daga Quraishawan Hijaz a matsayin shugaba.
Game da abin da ka rubuta cewa: ‘Ka miƙa mana masu kashe Usman,’ me ya haɗa ka da Usman? Kai mutum ne daga Banu Umayya, kuma ’ya’yan Usman sun fi ka cancanta da neman hakkinsa da fansar jininsa. Idan kana ganin ka fi su cancanta kuma ka fi su ƙarfi wajen ɗaukar fansar mahaifinsu, da farko ka yi min biyayya. Sannan ka kawo waɗannan mutane domin a gurfanar da su a gabana, ka kuma gabatar da ƙararka, domin in tilasta maka da su bin hanyar gaskiya.
Game da bambartawar da kayi tsakanin Sham da Basra, da tsakaninka da Talha da Zubair, gaskiyar lamari ɗaya ce. Mubaya’ata ta kasance ta gama-gari kuma ta shafi kowa. Ba ta karɓar sake dubawa, kuma ba za a sake buɗe haƙƙin zaɓe a cikinta ba.
Game da nuna tausayinka ga Usman da zarginka gare ni cewa na shiga cikin lamarinsa, ba ka faɗi wannan bisa bayyananniyar gaskiya ko tabbataccen ilimi ba.
Game da amincewarka da fifikona a Musulunci, da dangantakata da Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa), da martabata a tsakanin Quraishawa, wallahi, da kana iya musanta waɗannan darajoji, da ka musanta su ma.” [3]
Saɓani tsakanin Ashtar da Jarir
Bayan mutane sun soki Jarir, Ashtar ya je wajen Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya yi da’awar cewa da an tura shi, da ya iya mayar da Mu’awiya zuwa tafarki madaidaici. Jarir ya hana wannan mataki, yana mai nuni da haɗarin rai da yiwuwar a jingina masa zarge-zarge. Amma daga ƙarshe, Ashtar ya zargi Jarir da haifar da rarrabuwar kai da rusa tsarin sahabbai. [4]
Wasiƙar da Mu’awiya Ya Ji Tsoron a Karanta!
A cikin wasiƙar da Mu’awiya ya rubuta wa Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya lissafa matsayin mahaifinsa na sarauta a zamanin Jahiliyya, kuma ya ɗauki matsayinsa na shugaba a Musulunci, dangantakarsa da Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa), da kasancewarsa marubucin wahayi a matsayin alamar falalarsa.
Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya rubuta:
“Shin ɗan mai cin hanta yana zaluntar falalolina? Ya kai yaro, ka rubuta: Muhammad (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa), Annabi, ɗan’uwana ne kuma dangina ta aure. Na riga ku shiga tafarkin Musulunci tun ina saurayi, alhali kafin hakan, ina cikin cikin mahaifiyata, na tabbatar da Annabcinsa. Na kasance ina sallah tun ina ƙaramin yaro kafin in kai shekarun balaga. Kaico, kaico, kaico ga wanda gobe zai tsaya a gaban Allah tare da zaluncin da yayi mini!”
Bayan haka, Mu’awiya ya ce:
“Ku ɓoye wannan wasiƙa kada mutanen Sham su karanta ta, domin kada su karkata zuwa ga ɗan Abu Talib.” [5]
Cinikin Mu’awiya da Amr ɗan As
Mu’awiya ya nemi Amr ɗan As ya shiga Jihadi a kan Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), yana mai kawo hujjoji kamar saɓa wa umarnin Allah, haifar da rarrabuwar kai, kashe halifa, tayar da fitina da yanke zumunci.
Amr ya tambaya:
“Da wa?”
Lokacin da ya ji cewa Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ne, sai ya jaddada falalolin Jagoran Masu Taqawa, kamar Hijira, gabatarsa a Musulunci, kusancinsa da Manzon Allah, ilimi, fiqhu da matsayin da Allah Ya ba shi. Sannan ya tambayi abin da zai samu idan ya haɗa kai da Mu’awiya.
Mu’awiya yayi masa alkawarin mulkin Masar. Amr ya nemi a ba shi shi a matsayin rabonsa, amma Mu’awiya ya ɗan yi jinkiri kan wannan shawara. [6]
Sukar Jagoran Masu Taqawa ga Mummunan Haɗin Kai
Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ce a cikin wata huduba game da yarjejeniyar Amr ɗan As da Mu’awiya:
“Amr ɗan As bai yi wa Mu’awiya mubaya’a ba sai bayan ya sanya sharadin karɓar babban farashi a kan wannan mubaya’a. To, hannun mai yin wannan mubaya’a ya gaza, kuma amanar mai saya ta wulaƙanta. Yanzu da wutar wannan yaƙi ta ƙone kuma harshenta ya tashi, ku shirya kanku ku kuma tanadi kayan yaƙi. A wannan tafarki, ku raya haƙuri a cikin zukatanku, domin haƙuri da tsayin daka su ne hanya mafi kusa zuwa nasara.” [7]
Hujjar Mu’awiya domin Fara Yaƙi
Kafin tafiya zuwa Siffin, Mu’awiya ya rubuta wa mutanen Makka da Madina, yana kiran su zuwa ɗaukar fansar jinin Usman.
A cikin martaninsa ga Mu’awiya da Amr ɗan As, Abdullah ɗan Umar ya rubuta cewa:
“Kun bi hanyar da ba daidai ba. Kai, Mu’awiya, ɗaya ne daga cikin waɗanda Annabi ya ’yanta, kai kuma, Amr, wanda ake zargi ne. Ku bar mu, domin ba ku da wani mataimaki ko waliyyi a wajenmu.”
Sa’d ɗan Abu Waqqas ma ya amsa cewa duk waɗanda suka kasance cikin majalisar Umar suna daga cikin waɗanda halifanci ya halatta gare su, kuma babu wanda ya fi wani sai da ijma’i. Amma Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana da duk falalolin da muke da su, alhali mu ba mu da abin da yake da shi.
Sannan ya ƙara da cewa da Talha da Zubair sun zauna a gidajensu, da ya fi alheri a gare su. [8]
Bayar da Umarnin Jihadi
Kafin tafiya daga Kufa zuwa Siffin, Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi jawabi ya ce:
“Abin mamaki ne game da Mu’awiya ɗan Abu Sufyan, wanda yake jayayya da ni a kan halifanci kuma yake musanta Imamanci na. Yana ganin cewa ya fi ni cancanta, alhali da wannan tunanin batanci ya yi wa Allah da Manzonsa rashin kunya. Ba shi da haƙƙi ko hujja, Muhajirai ba suyi masa mubaya’a ba, kuma Ansar da sauran Musulmi ba su miƙa wuya gare shi ba.
Ya ku Muhajirai, ya ku Ansar, da duk masu jin maganata! Ashe ba ku ɗauki biyayya gare ni a matsayin wajibi a kanku ba? Ashe ba ku yi mini mubaya’a cikin yardar rai da cikakken niyya ba, ni kuma na karɓi alkawari daga gare ku cewa za ku karɓi maganata? Ashe a wannan ranar mubaya’arku gare ni ba ta fi mubaya’ar Abu Bakr da Umar ƙarfi ba? To me ya sa ba su warware mubaya’ar halifofin da suka gabata ba, amma suka karya alkawarina kuma ba su cika alƙawarina ba?
Ashe ba wajibi ne a kaina in yi muku nasiha kuma in nace kan aiwatar da alhaki ba? Ashe ba ku san cewa mubaya’a gare ni wajibi ce a kanku, ko kuna gabana ko kuna nesa da ni ba?
Ta yaya Mu’awiya da mabiyansa suka karya alkawarina, alhali ni, saboda dangantakata, kusancina da tarihin imanina a wajen Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa), na fi kowa cancanta da halifanci? Shin kun manta da maganar Manzon Allah a ranar Ghadir? Shin kun manta da abin da ya faɗa game da Wilayata da ƙaunata?
To ku ji tsoron Allah, ku kuma shirya domin Jihadi da Mu’awiya, wanda ya karya alkawarinsa gare ni kuma ya fitar da mabiyansa daga biyayyata.” [9]
Dalilin Jagoran Masu Taqawa na Jinkirta Fara Yaƙi
Lokacin da sahabbansa suka yi masa ƙorafi cewa me ya sa bai fara yaƙi ba, Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ce:
“Game da abin da kuke faɗa cewa duk wannan jinkiri ya samo asali ne daga tsoron mutuwa, wallahi, babu bambanci a gare ni ko ni zan je wajen mutuwa, ko mutuwa za ta zo wajena.
Game da abin da kuke faɗa cewa ina shakka game da mutanen Sham, wallahi, ban taɓa jinkirta yaƙi ba sai saboda fatan cewa wata ƙungiya daga cikinsu za ta haɗu da ni, ta samu shiriya ta wurina, kuma ta sami haske daga haskena. Wannan ya fi soyuwa a gare ni fiye da in kashe su suna cikin ɓatarsu, ko da yake a ƙarshe za su koma suna ɗauke da nauyin zunubansu.” [10]
Jihadin Bayyanawa a Gaban Fitinar Mu’awiya
Ta hanyar kulawa da rubuce-rubuce da wasiƙun hujja ga Mu’awiya cikin tsari mai kyau, Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana neman bayyana gaskiya da kuma kiyaye tsarin siyasa a cikin al’ummar Musulmi.
Sulaym, wanda yake daga cikin amintattun sahabban Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya ce:
“A lokacin Yaƙin Siffin, Mu’awiya ya aika da saƙonsa zuwa ga Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ta hannun Abu Darda da Abu Huraira. Bayan Imam ya ji saƙon kuma ya karanta wasiƙar, ya rubuta wa Mu’awiya cikakkiyar amsa mai tsawo.”
Jagoran Masu Taqawa ya ce:
“Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya naɗa ni a Ghadir Khumm, ya ce:
‘Allah Ya ɗora mini wani saƙo da ya matse kirjina, domin ina zaton mutane za su ƙaryata ni. Amma Allah Yayi mini gargaɗi cewa idan ban isar da shi ba, Za a azabtar da ni. Ya Ali, ka tashi!’
Sannan ya yi kiran sallar jama’a, ya yi sallar Azuhur tare da mutane. Bayan haka ya ce:
‘Ya ku mutane! Allah ne Mai iko da ni, ni kuma mai iko ne a kan muminai, kuma iko na a kansu ya fi ikon da suke da shi a kan kansu. Ku sani, duk wanda nake shugaban sa , Ali ma shugaban sa ne. Ya Allah! Ka so wanda ya so shi, Kayi gaba da wanda yayi gaba da shi, Ka taimaki wanda ya taimake shi, kuma Ka wulaƙanta wanda ya wulaƙanta shi.’
Sai Salman Bafarisi ya tashi ya ce:
‘Ya Manzon Allah! Yaya Wilayarsa take?’
Manzon Allah ya ce:
‘Wilayarsa kamar Wilayata ce. Duk wanda na fi shi cancanta da kansa, Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ma ya fi shi cancanta da kansa.’
Sai Allah Maɗaukaki Ya saukar da wannan aya:
«اليَومَ أكمَلتُ لَكُم دينَكُم و أتمَمتُ عَلَيكُم نِعمَتي و رَضيتُ لَكُمُ الإسلامَ ديناً»
‘A yau Na kammala muku addininku, kuma Na cika muku ni’imata, kuma Na yarda da Musulunci a matsayin addininku.’
Salman Bafarisi ya tambaya:
‘Ya Manzon Allah! Shin waɗannan ayoyi sun sauka ne game da Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) kaɗai?’
Cikamakin Annabawa (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya ce:
‘Sun sauka game da shi da magadansa har zuwa Ranar Qiyama.’
Sannan ya ce:
‘Ya Salman! Kai da waɗanda suke tare da kai a wannan majalisa ku zama shaida, kuma ku isar da wannan labari ga waɗanda ba sa nan.’
Salman ya ce:
‘Ya Manzon Allah! Ka bayyana mana su.’
Cikamakin Annabawa (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya ce:
‘Ali ɗan’uwana ne, wazirina, wasiyyina, magajina, halifana a cikin al’umma, kuma mai iko da kowane mumini bayana. Bayansa za a samu Imamai goma sha ɗaya daga zuriyarsa: na farko Hassan, sannan Husseini, bayan haka mutum tara daga zuriyar Husseini, ɗaya bayan ɗaya. Su suna tare da Al-Qur’ani, kuma Al-Qur’ani yana tare da su. Ba za su rabu ba har sai sun iso gare ni a bakin Tafkin Kawthar.’” [11]
Dabarar Yaudarar Amr ɗan As
Lokacin da Mu’awiya yaji labarin motsin rundunar Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), sai ya ji tsoron shan kaye, ya nemi shawarar Amr ɗan As.
Amr, bayan yayi nazarin bambancin yanayin yaƙin Ali da na Mu’awiya, ya ba da shawarar a yi amfani da dabarar “kira zuwa Al-Qur’ani” domin hana shan kaye. Ya ba da shawarar a ɗaga Al-Qur’ani a kan māsuna domin a haifar da ruɗani da rarrabuwar kai a cikin rundunar, har ta kai ko da sun amince da kiran, tsarin su ya rushe. [12]
Makircin Rundunar Sham
Tamim ɗan Hudhaym ya ruwaito cewa da sassafe, rundunar Sham ta rataye Al-Qur’ani a kan māsuna. A cikinsu, mafi girman Al-Qur’ani an ɗora shi a kan māsuna uku, kuma mutum goma ne suke ɗauke da shi. [13]
Amsa ga Makircin Mu’awiya
Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya rubuta wa Mu’awiya:
“Abubuwan da suke isa gare ni daga gare ka suna ban mamaki! Na san sarai inda tafarkinka zai kai ka da yadda ƙarshen ka zai kasance. Idan ban gaggauta a kanka ba, ba saboda gazawa ba ne; saboda wani lokaci ne da na yi imani da shi, alhali kai ba ka yarda da shi. Kamar ina ganinka kana kuka saboda tsananin yaƙi, mabiyanka kuma, saboda tsoron takobi, suna kirana in amince da Littafin da su kansu ba su yi imani da shi ba kuma suna musanta shi.” [14]
Tsawatar wa Sahabbai da Aka Yaudara
Lokacin da sahabbansa suka koma daga yaƙi a Siffin bayan makircin Mu’awiya na ɗaga Al-Qur’ani, Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ce:
“Lallai kun aikata wani abu da ya raunana ginshiƙan Musulunci, ya rushe martabarsa, kuma ya sanya ku cikin rauni da wulaƙanci.
Ku ne kuke da fifiko, kuma abokan gaba suna tsoron halaka. Haka kuma, yawan waɗanda aka kashe daga cikinsu yayi musu nauyi, kuma sun ɗanɗani azabar raunuka. Sai suka ɗaga Al-Qur’ani, suka kira ku zuwa abin da ke cikinsa domin su hana ku kai musu hari, su katse yaƙi tsakaninku, kuma su yi muku kwanton mutuwa ta hanyar makirci da yaudara.
Idan kun yarda da su a kan abin da suke so, kuma kun ba su abin da suka nema, to lallai an yaudare ku. Wallahi, bana zaton bayan wannan za ku sake bi na a tafarkin shiriya da gaskiya, ko ku gane ingantacciyar dabara.” [15]
Bayyana Rashin Yarda da Lamarin Sasantawa
Bayan an rubuta yarjejeniyar sulhu da sasantawa, lokacin da mutanen Iraq suka zarge shi, Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ce:
“Wallahi, ban yarda da wannan lamari ba, kuma ban so ku yarda da shi ba. Amma saboda ba ku amince da komai ba sai yarda da shi, ni ma na yarda. Bayan an yarda, ba ya halatta a koma baya, domin bayan tabbatarwa, ba ya halatta a sauya matsaya; sai dai idan mutum ya saɓa wa Allah ta hanyar karya alkawari, kuma ya keta Littafinsa ta hanyar warware yarjejeniya. A wannan lokacin, ku yaƙi waɗanda suka bar umarnin Allah.
Game da abin da kuka faɗa kan Ashtar, cewa ya ƙi bin umarnina kuma ya saɓa mini da hannunsa wajen rubuta wasiƙar, shi ba ya cikin waɗancan masu tawaye, kuma bana jin tsoronsa a wannan lamari.
Da a ce akwai mutum biyu kamar shi a cikinku; kai, da a ce ko mutum ɗaya irin sa yana cikinku, wanda yake ganin abin da yake faruwa ga maƙiyinku kamar yadda shi yake gani. Da wahalar al’amarinku a kaina ta ragu, kuma da na yi fatan wasu daga cikin karkacewarku za su daidaita.
Na hana ku abin da kuka aikata, amma kuka saɓa mini. Don haka ni da ku mun zama kamar maganar wani mutum daga Hawazin wanda ya ce:
‘Ashe ni ba na cikin ƙabilar Ghaziyya ba? Idan suka ɓace, ni ma zan ɓace; idan kuma Ghaziyya ta samu shiriya, ni ma zan samu shiriya.’” [16]
Majiyoyi
[1] Bihar al-Anwar, juzu’i na 32, shafi na 378.
[2] Bihar al-Anwar, juzu’i na 32, shafi na 378.
[3] Bihar al-Anwar, juzu’i na 32, shafi na 379.
[4] Waq’at Siffin, juzu’i na 1, shafi na 59.
[5] Bihar al-Anwar, juzu’i na 33, shafi na 132.
[6] Bihar al-Anwar, juzu’i na 32, shafi na 373.
[7] Nahjul Balagha, Huduba ta 26.
[8] Bihar al-Anwar, juzu’i na 32, shafi na 382.
[9] Bihar al-Anwar, juzu’i na 32, shafi na 388.
[10] Bihar al-Anwar, juzu’i na 32, shafi na 556.
[11] Kitab Sulaym ɗan Qais, shafi na 142.
[12] Kitab Sulaym ɗan Qais al-Hilali, shafi na 177.
[13] Bihar al-Anwar, juzu’i na 32, shafi na 529.
[14] Bihar al-Anwar, juzu’i na 33, shafi na 124.
[15] Al-Kamil fi al-Tarikh, juzu’i na 3, shafi na 322; Al-Irshad, juzu’i na 1, shafi na 268.
[16] Al-Irshad, juzu’i na 1, shafi na 269.