Most searched:

Imam Husseini Ya Yi Alfahari da Jagoran Masu Taqawa a Ranar Ashura

Imam Husseini (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), a cikin baitukan rajaz da ya rera a ranar Ashura, ya yi alfahari da tsarkakakken asalinsa. Ya gabatar da Amirul Muuminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a matsayin misali marar tamka na jarumta, adalci da imani, inda ya bayyana fifikon ruhaniya, ɗabi’a da na ma’anawi na iyalan Ahlul Baiti.

Rajaz wani nau’in waƙa ne da jarumai da mayaƙa suke rerawa a farkon yaƙi. A ranar Ashura ma, sahabban Imam Husseini (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da shi kansa Imam sun shiga fagen daga suna rera baitukan rajaz waɗanda aka ruwaito a littattafan da suka yi bayani kan shahadar Imam Husseini.

Waɗannan baitukan rajaz, ƙari da ƙarfafa zukatan sahabbai, sun bayyana zaluncin da aka yiwa gaskiya da matsayin Imam . Haka kuma sun nuna dangantakar biyayya ga ƙa’idojin Allah da darajoji na Amirul Mu’uminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cikin salo na jarumta.

Me Ya Sa Ake Rera Rajaz?

Babban kuma mafi yawan amfanin rajaz a fagagen yaƙi shi ne mayaƙi ya gabatar da kansa ga wanda zai fafata dashi da kuma ga rundunar maƙiya.

Amfani na biyu na rajaz shi ne bayyana nasaba da martabar mayaƙi, wanda yake yin alfahari dasu kuma yake nuna fifikonsa a gaban maƙiyi.

Da yammacin ranar Ashura, Imam Husseini (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi bankwana da Ahlul Baitinsa sannan ya nufi fagen yaƙi. Yana rera wani dogon rajaz mai cike da ƙarfi da jarumta yana kuma yaƙi.

Bayyana Sansanin Kafirci

Imam Husseini (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), a cikin rajaz dinsa, yayi nuni da jarumtar Ahlul Baiti da kuma rashin adalcin ƙiyayyar da aka nuna wa Amirul Mu’uminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ’ya’yansa. Haka kuma ya bayyana yadda tafarkin Ashura yake da alaƙa da neman gaskiya da adalcin Jagoran Masu Taqawa.

A ranar Ashura, kafin Imam Husseini (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya shiga fagen yaƙi, ya ce:

“Waɗannan mutane sun karkata zuwa kafirci kuma sun juya baya ga ladan Allah, Ubangijin talikai. Tun kafin wannan, mahaifina Imam Ali (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ɗan’uwana Imam Hassan (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), waɗannan manyan misalai na ɗaukaka da karamci, sun kasance abin ƙiyayyarsu. Yanzu ma, cikin gaba da ƙiyayya, sun yanke shawarar kai min hari.

Kaicon waɗannan ƙasƙantattun mutane waɗanda suka tara rundunarsu domin fuskantar Ahlul Baitin Cikamakin Annabawa. Sun yi wa juna alkawari su zubar da jinina domin neman yardar wasu mutane biyu mugaye. A wannan tafarki, domin faranta ran Ubaidullah, ɗan wata muguwar mace, basu ji tsoro ko kaɗan daga fushin Allah ba. Umar ɗan Sa’ad ma cikin zalunci ya sanya ni a matsayin abin kai hari ga rundunarsa; rundunar da ta kwararo daga kowane gefe kamar ambaliyar ruwa.”

Alfahari da Nasaba

A wani ɓangare na rajaz dinsa, Imam Husseini (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yayi nuni da babban matsayin Amirul Mu’uminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya gabatar dashi a matsayin magajin Annabawa, gwarzon yaƙe-yaƙe kuma abokin Cikamakin Annabawa a mawuyacin lokuta. Haka kuma, ta hanyar tunatar da dangantakarsa ta iyali da kusancinsa da Manzon Allah da Sayyada Zahra (Amincin Allah ya tabbata a gare ta), ya jaddada ɗaukakar asalinsa.

Imam Husseini (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ce:

“Ba ni da wani laifi sai alfahari da hasken taurari biyu na Farqad, taurarin da ake amfani dasu wajen gano hanya cikin dare. Ɗaya shi ne Amirul Mu’uminiin Imam Ali (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), mutumin kirki bayan Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa), ɗayan kuma shi ne Cikamakin Annabawa, wanda yake daga Quraysh kuma ɗan asalin Quraysh.

Zaɓaɓɓun bayin Allah su ne mahaifina da mahaifiyata, kuma ni ɗansu ne, kamar azurfar da aka samo daga tsantsar zinariya. Ni azurfa ne kuma ɗan lu’ulu’u biyu tsarkaka. Mahaifiyata Sayyada Fadima Zahra (Amincin Allah ya tabbata a gare ta) ce, mahaifina kuma magajin Annabawa ne, shugaban aljanu da mutane.

Shi ne wanda ya kafa tarihin jarumta a yaƙe-yaƙen Badr, Uhud da Hunain, ya kuma rinjayi jarumai. A Yaƙin Uhud, da jarumtarsa ya kwantar da zukata, ya karya rundunar maƙiya; a Yaƙin Ahzab, Fatahu Makka da sauran fagage kuma ya kasance mai taimakon muminai.

Shi ne wanda yayi nasara a Khaybar, wanda ya soki zuciyar maƙiyi da takobinsa mai kaifi biyu, ya kuma tarwatsa sahunsu. Wannan babban mutum ne ya halaka rundunonin maƙiya a tafarkin Allah, waɗanda suka taru domin ɗaukar fansa a Hunain.

Amma me wannan al’umma marar godiya ta yi wa zuriyar nan biyu? Tsarkakakkiyar zuriyar Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) da iyalan Amirul Mu’uminiin Imam Ali (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), gwarzon fagagen yaƙi.

Wa yake da kawu irin Ja’afar? Ja’afar wanda Allah Ya ba shi fikafikai biyu. Wa yake da kaka irin Cikamakin Annabawa, da babban jagora kamar Amirul Mu’uminiin Imam Ali (Amincin Allah ya tabbata a gare shi)? Ni ɗan waɗannan manyan abin koyin bil’adaman ne.

Mahaifina kamar rana ne, mahaifiyata kamar wata, ni kuma tauraro ne da aka haifa daga hasken wata da rana. Kakana Manzon Allah ne, fitilar shiryarwar bil’adama. Mahaifina mai girma shi ne wanda ya tsaya daram a dukkan mubaya’o’i biyu.”

Alfahari da Jagoran Masu Taqawa

A wani ɓangare na rajaz dinsa, Imam Husseini (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), yayin bayyana Amirul Mu’uminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya siffanta shi a matsayin zaki jarumi a fagen yaƙi da kuma wata taska mai daraja ta Ahlul Baiti. Haka kuma ya jaddada rawar Ahlul Baiti wajen shiryar da mutane da kuma babban matsayin Shi’arsu a wajen Allah.

Imam Husseini (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi kira a fagen yaƙi yana cewa:

“Amirul Mu’uminiin Imam Ali (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) jarumi ne kuma gwarzo, mai ƙarfin zuciya, mai girma, mai karimci kuma mai ƙarfi. Shi ne igiya mai ƙarfi ta addini; Amirul Mu’uminiin (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), mai tafkin Kausar kuma wanda yayi sallah yana fuskantar alƙibla biyu.

Tun yana ɗan shekara bakwai yake yin ibada tare da Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa), a lokacin da babu wani mutum a doron ƙasa da yake yin sallah sai su biyun. Tun daga lokacin da ya buɗe idonsa zuwa duniya, ya juya baya ga gumaka kuma bai taɓa yin sujada ga gumaka tare da Quraysh ko sau ɗaya ba. A zamanin da dukkan Quraysh suke bautar gumaka, shi yana ƙuruciyarsa da samartakarsa yana bautar Allah Makaɗaici kaɗai.

Mahaifina zaki ne a filin jarumta; yana riƙe da mashi yana kai duka mai hallakarwa ta kowane gefe. Tafiyarsa tana da ƙarfi kamar ta zaki, amma maƙiya masu ƙiyayya sun aika dukkan waɗannan mutanen ɗaya bayan ɗaya zuwa mutuwa.

Ni ɗan Amirul Mu’uminiin Imam Ali (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ne, mutumin kirki daga gidan Hashim. Idan zan faɗi abubuwan da nake alfahari dasu, ya ishe ni cewa kakana Manzon Allah ne, mafificin halittun Allah. Mu ne masu haskaka doron ƙasa kuma fitilun shiryarwarsa.

Mahaifiyata Sayyada Fadima (Amincin Allah ya tabbata a gare ta) ce, daga tsarkakakkiyar zuriyar Ahmad (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa), kawuna Ja’afar kuma shi ne ma’abucin fikafikai biyu. Ayoyin gaskiya na Al-Qur’ani sun sauka game damu, kuma shiriyar Allah tana gudana a tsakaninmu.

Wahyin Allah koyaushe yana ambatonmu da alheri. Mu amana ce daga Allah ga dukkan mutanen duniya, kuma mun bayyana wannan gaskiya a kowane hali.

Alhakin wannan tafki yana hannunmu, kuma za mu shayar da masoyanmu da kofin Manzon Allah; wannan gaskiya ce da ba za a iya musantawa ba.

Shi’armu su ne mafi daraja a tsakanin mutane, maƙiyanmu kuma a Ranar Qiyama ba za su samu komai ba sai asara.”

Madogara
Al-Manaqib, juzu’i na 4, shafi na 79.

Ƙarin abubuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *