An haifi Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) a ranar 17 ga Rabi’ul Awwal a shekarar Giwaye, a Makka, daga mahaifi mai suna «Abdullah ɗan Abdulmuɗallib» daga kuma mahaifiya mai suna «Amina ’yar Wahab».
Amirul Mu’uminin (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bayyana abubuwan ban mamaki da sauye-sauyen duniyar halitta da suka faru a daren haihuwar Cikamakin Annabawa (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) kamar haka: «A lokacin da aka haifi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa), gumakan Ka’aba suka fāɗi, kuma da dare ya shiga sai aka ji wata murya daga sama tana cewa: «جاءَ الحَقُّ و زَهَقَ الباطِلُ إنَّ الباطِلَ کانَ زَهوقاً،» Gaskiya ta zo, ƙarya kuwa ta gushe; lalle ƙarya mai gushewa ce.» (Suratul Isra’i, aya ta 81). A wannan dare, haske ya mamaye duniya gaba ɗaya, duwatsu, tsakuwa da itatuwa suyi kamar suna dariya, kuma dukkan halittun da suke cikin ƙasa da sama suka fara yin tasbihin Allah. A wannan lokacin kuma, Shaiɗan ya gudu yana ihu yana cewa: «Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) shi ne mafi alherin al’umma, mafificin halitta, mafi darajar bawa kuma mafi girman mutum a cikin talikai.» [1]
Haɗin Har Abada da Kaske Ɗaya
Matsayi mai ɗaukaka da hakikanin haske na Cikamakin Annabawa (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) da Amirul Mu’uminin (amincin Allah ya tabbata a gare shi) a tsarin halitta suna nuna wata alaƙa ta har abada wadda ba ta yankewa. Waɗannan manyan hakika suna bayyana asalin kasancewar Ahlul Baiti da kuma tushen shiriya da imanin mabiyansu na gaskiya.
Haɗin har abada da haɗin haske ɗaya tsakanin Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) da Amirul Mu’uminina (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya wanzu tun kafin a halicci mutum. Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya ce game da haka: «Ni da Ali mun kasance haske ɗaya a gaban Allah, muna yin tasbihi da tsarkake Haƙƙi shekaru dubu goma sha huɗu kafin a halicci Adam. Lokacin da Allah Ya halicci Adam, Ya sanya wannan hasken a cikin tsatsonsa, kuma mun ci gaba da kasancewa cikin jiki ɗaya har sai da muka rabu a cikin tsatson Abdul’muɗallib; annabta ta kasance tawa, khalifanci kuma ya zama na Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi).» [2]
Mahaliccin duniya Ya halicci Ahlul Baiti da mabiyansu daga tushe guda na haske. Jabir ɗan Abdullah al-Ansari ya ruwaito daga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) cewa ya ce: «Allah Maɗaukaki Ya halicce ni, Ali ɗan Abu Ɗalib, Fadima, Hassan da Hussaini (amincin Allah ya tabbata a gare su) daga haske guda. Sa’an nan Ya haɗa wannan haske, Ya halicci Shi’armu daga gare shi. Saboda haka, mu muka yi wa Allah tasbihi, Shi’armu suma suka yi tasbihi; mu muka tsarkake Shi, Shi’armu suma suka tsarkake Shi.» [3]
Haɗin kasancewa da kamanceceniya tsakanin hakikanin annabta da imamanci a tsakanin Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) da Amirul Mu’uminina (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bayyana a sarari. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya kuma ce: «Ni da Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi) mun fito daga haske guda ne; ni da shi muna daga hakika guda ne. Shi daga gare ni yake, ni kuma daga gare shi nake. Namansa namana ne, jininsa kuma jinina ne. Abin da ke sa shi baƙin ciki yana ba sani baƙin ciki, abin da kuma ke sani baƙin ciki yana sa shi baƙin ciki.» [4]
Ci gaban haske Ɗaya a Tafarkin Ceto
Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa), wanda shi kansa bayyanar «جاء الحق» ne kuma mafarar zamanin gushewar ƙarya ne, a cikin rikice-rikicen fitina bayan rasuwarsa, ya ɗaure hannun Ammar Yasir da igiyar wilayar Sarkin Masu Taƙawa; domin su biyun haske ɗaya ne wanda ke ganin ci gaba da shiriya da ceton al’umma ya ta’allaka ne ga bin tafarkin Amirul Mu’uminina (amincin Allah ya tabbata a gare shi).
Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa), saboda sanin fitinun da za su biyo bayansa, ya kira Ammar Yasir zuwa ga riƙo da Amirul Mu’uminina (amincin Allah ya tabbata a gare shi). Ya ce: «Ya kai Ammar! Bayan ni za a samu fitintinu da rikice-rikice, har takobin saɓani zai riƙa yawo tsakanin al’umma, wasu daga cikinsu su kashe wasu, wasu kuma su barranta daga wasu. Idan ka ga wannan yanayi, ka bi wannan mutum mai aske kai wanda yake a gefen dama na, wato Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi)! Idan dukan mutane suka bi wata hanya, Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi) kuma ya bi wata hanya, to ka bi hanyar Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi), ka bar mutane; domin Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ba zai taɓa kawar da kai daga tafarkin shiriya ba. Ka sani cewa biyayya ga Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi) biyayya ce gare ni, kuma biyayya gare ni biyayya ce ga Allah.» [5]
Matsayi mai ɗaukaka na Amirul Mu’uminina (amincin Allah ya tabbata a gare shi) a gefen Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya wuce iyakar abota, ya kuma haɗu da tushen imani, ibada da cikakkiyar taƙawa. Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya ce game da ƙaunar Sarkin Masu Taƙawa: «Ƙaunar Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi) kyakkyawan aiki ne mai ɗorewa wanda babu wani zunubi da zai cutar tare da shi, kuma ƙiyayya gare shi sharri ce wadda babu wani kyakkyawan aiki da zai amfana tare da ita.» [6]
Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya ce game da wilayar Amirul Mu’uminina (amincin Allah ya tabbata a gare shi): «Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ƙofar gafara ne; duk wanda ya shiga ta cikinta mumini ne, duk wanda kuma ya fita daga cikinta kafiri ne.» [7]
Abu Zarr ya ruwaito cewa Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya kwatanta matsayin Amirul Mu’uminina a cikin al’umma da Ka’aba. Ya ce: «Misalin Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi) a cikin wannan al’umma kamar Ka’aba ce mai sutura; kallonta ibada ce, kuma nufarta wajibi ne.» [8]
Imam Baqir (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ruwaito daga iyayensa game da mafiya falala a cikin mutane cewa an tambayi Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa): «Wane ne mafi alherin mutane?» Ya ce: «Mafi alheri, mafi yawan taƙawa kuma mafi kusa da Aljanna a cikin mutane shi ne wanda ya fi kusa da ni; kuma a cikinku babu wanda ya fi Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi) taƙawa da kusanci gare ni.» [9]
Sarkin Masu Taƙawa; Khalifa kuma Mai Ci Gaban Tafarkin Annabta
Naɗa matsayin imamanci da khalifancin Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ga Amirul Mu’uminin (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya samo asali ne daga tsarin Allah da zaɓin azali ne. Wannan babban matsayi na wilaya ita ce hanya kaɗai ta tsira daga ɓata, kuma ita ce mafi ƙarfi daga cikin alaƙar da ke tsakanin bayi da alkawuran Allah. Bayyanar matsayin wazirin Annabi da mataimakinsa a Al’ Arshi da Sidratul Muntaha na nuna alaƙar da ba ta yankewa tsakanin annabta da imamanci a tsarin halitta.
Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya ce: «Allah Ya sanya zuriyar kowane annabi a bayan sa, amma Ya sanya zuriyata a bayan Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi).» [10]
A cikin tunanin annabci, Sarkin Masu Taƙawa shi ne halifansa na gaskiya. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya bayyana wannan alaƙa da cewa: «Shi mataimakina ne, wazirina ne kuma halifana ne a cikin iyalina. Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi) shi ne mafi alherin wanda zan bari a bayana; shi ne zai cika alkawurana kuma ya biya bashina.» [11]
Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya ce game da alkawari da Sarkin Masu Taƙawa: «Muddin kuna cikin wilayar Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi), ba za ku ɓace ko ku halaka ba. Idan kuka saɓa masa, kurakuranku da son zuciyarku za su kai ku ga ɓata. Ku ji tsoron Allah game da alkawarinsa, domin Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi) shi ne alkawarin Allah a cikinku.» [12]
Ibn Abbas ya ruwaito game da khalifancin Annabi cewa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya kama hannun Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi), sannan ya yi sallar raka’a huɗu. Bayan haka ya ɗaga hannuwansa yana addu’a: «Ya Allah! Kamar yadda Musa ɗan Imran ya roƙe Ka, ni ma ina roƙonKa Ka buɗe mini ƙirjina, Ka sauƙaƙa mini al’amari na, Ka warware mini ƙulli dake harshena domin su fahimci maganata, kuma Ka sanya mini waziri daga iyalina, wato ɗan’uwana Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi); Ka ƙarfafa bayana da shi, kuma Ka sanya shi abokin tarayya na cikin al’amarina.» [13]
Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya ce game da halifansa: «Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi) shi ne mafi alherin wanda zan bari a bayana; shi ne wanda zai biya bashina kuma ya cika alkawurana.» [14]
Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya ambaci fitattun siffofin Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi) a cikin wata ruwaya. Ya ce: «Ya Ali! Allah Ya dubi talikai, sannan Ya zaɓe ni daga cikinsu, Ya fifita ni a kan mazajen talikai. Sa’an nan Ya sake dubawa karo na biyu, Ya zaɓe ka daga cikinsu, Ya fifita ka a kan mazajen talikai. Sa’an nan Ya dubi karo na uku, Ya zaɓi Imamai daga zuriyarka a kan mazajen talikai. Sa’an nan Ya dubi karo na huɗu, Ya zaɓi Fadima (aminci ya tabbata a gare ta) a kan matan talikai. Ya Ali! Na ga sunanka tare da sunana a wurare uku, kuma hakan ya ba ni kwanciyar hankali:
۱. A Mi’iraji, lokacin da na isa Baitul-Muqaddas aka ɗaga ni zuwa sama, sai na ga a kan dutsen wurin an rubuta: «Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) Manzonsa ne; Na ƙarfafa shi da wazirinsa, kuma Na taimake shi ta hanyar wazirinsa.» Sai na ce wa Jibrilu (amincin Allah ya tabbata a gare shi): Wane ne wazirina? Jibrilu ya ce: «Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi).»
۲. Lokacin da na isa Sidratul Muntaha, sai na ga an rubuta a kanta: «Lalle Ni ne Allah; babu abin bautawa sai Ni, kuma Ni kaɗai. Muhammad zaɓaɓɓena ne daga cikin halittuna; Na ƙarfafa shi da wazirinsa, kuma Na taimake shi ta hanyar wazirinsa.» Sai na ce wa Jibrilu (amincin Allah ya tabbata a gare shi): «Wane ne wazirina?» Sai ya amsa: «Ali ɗan Abu Ɗalib (amincin Allah ya tabbata a gare shi).»
۳. Lokacin da na wuce Sidratul Muntaha na isa Al’ Arshin Ubangijin talikai, sai na ga an rubuta a kan ginshiƙan Al’ Arshi: «Lalle Ni ne Allah; babu abin bautawa sai Ni, kuma Ni kaɗai. Muhammad ƙaunataccena ne kuma masoyina; Na ƙarfafa shi da wazirinsa, kuma Na taimake shi ta hanyar wazirinsa.» [15]
Majiyoyi:
[1] Bihar al-Anwar, Juzu’i na 15, shafi na 274
[2] Manaqib Ibn al-Maghazili, shafi na 88; Tarikh Dimashq, Juzu’i na 42, shafi na 67; al-Manaqib al-Khwarazmi, shafi na 145; Sharh al-Akhbar, Juzu’i na 1, shafi na 220; Ilal al-Shara’i, shafi na 134
[3] Kashf al-Ghumma, Juzu’i na 1, shafi na 458; Bihar al-Anwar, Juzu’i na 27, shafi na 131
[4] Awali al-La’ali, Juzu’i na 4, shafi na 124
[5] al-Umdah, Juzu’i na 1, shafi na 450
[6] al-Manaqib Ibn Shahrashub, Juzu’i na 3, shafi na 197; Kashf al-Ghumma, Juzu’i na 1, shafi na 93; Kashf al-Yaqin, Juzu’i na 1, shafi na 225; Irshad al-Qulub, Juzu’i na 2, shafi na 234; Bihar al-Anwar, Juzu’i na 39, shafi na 248; al-Fadha’il, Juzu’i na 1, shafi na 96; Awali al-La’ali, Juzu’i na 4, shafi na 86; al-Manaqib al-Khwarazmi, Juzu’i na 1, shafi na 76; Yanabi al-Mawadda, Juzu’i na 1, shafi na 375
[7] al-Sawa’iq al-Muhriqa, shafi na 125
[8] Tarikh Dimashq, Juzu’i na 42, shafi na 356; al-Manaqib Ibn Maghazili, shafi na 107
[9] Yanabi al-Mawadda, Juzu’i na 2, shafi na 274
[10] al-Mu’jam al-Kabir, Juzu’i na 3, shafi na 44
[11] Tarikh Dimashq, Juzu’i na 42, shafi na 57
[12] Yanabi al-Mawadda, Juzu’i na 2, shafi na 285; Ihqaq al-Haqq, Juzu’i na 6, shafi na 57
[13] al-Manaqib Ibn Maghazili, shafi na 389
[14] Tarikh Dimashq, Juzu’i na 42, shafi na 57
[15] Man La Yahduruhu al-Faqih, Juzu’i na 4, shafi na 374