Sashen Hulɗa da Jama’a na Atabutul Alawiyya, a daidai lokacin tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) da Imam Jaafar As-Sadiq (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya ba wasu jariran da aka haifa a asibitocin jahar Najaf al-Ashraf kyaututtuka.
Karrar al-Musawi, shugaban Sashin Hulɗar Cikin Gida, ya bayyana a wata hira da Cibiyar Labarai cewa: “A cikin shirye-shiryen Makon Sadiqain na Duniya karo na biyar, Atabutul Alawiyya ta taya iyalan jariran da aka haifa murna tare da ba su kyaututtuka.”
Al-Musawi ya ƙara da cewa: “Wata tawaga daga Atabutul Alawiyya ta ziyarci wasu asibitoci a tsakiyar birnin Najaf al-Ashraf, inda ta gana da iyalan da aka haifa musu jarirai domin ta yi murna tare dasu. An gudanar da wannan shiri tare da haɗin gwiwar sassan Harkokin Addini, Motoci da Yaɗa Labarai.”
Abin lura shi ne, an gudanar da wannan yunƙuri a cikin shirye-shiryen Makon Sadiqain na Duniya karo na biyar. Atabutul Alawiyya tana gudanar da wannan mako shekara ta biyar a jere, kuma ya ƙunshi shirye-shirye da ayyuka daban-daban na addini, al’adu da zamantakewa.










