Mai kula da Atabutul Alawiyya, wanda Hukumar Ilimi ta Alawiyya ta wakilta, ya buɗe rukunin Makarantun Atabatul Alawiyya a daidai lokacin gudanar da shirye-shiryen Makon Sadiqain. Ana gudanar da waɗannan shirye-shirye ne domin tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) da kuma jikansa mai girma, Imam Ja’far As-Sadiq (Amincin Allah ya tabbata gare shi). An gudanar da buɗewar ne tare da halartar wasu jami’an gwamnati da wakilan ɓangaren ilimi, jami’o’i da al’umma.
An gudanar da bikin buɗe rukunin tare da halartar Yusuf Kanawi, Gwamnan Najaf Ashraf, Hussein al-Isawi, Shugaban Majalisar Jaha, da kuma ƙarƙashin kulawa tare da halartar Ihsan Da’i, Mataimakin Mai Kula da Haramin Imam Ali. Haka kuma, mambobin kwamitin gudanarwa da shugabannin sassa daban-daban sun halarci bikin.
An fara bikin da jawabin Mai Kula da Haramin Imam Ali, wanda Mustafa Muni, mamba a kwamitin gudanarwa, ya karanta. A cikin jawabin, ya jaddada muhimmancin ilimi da rawar da yake takawa wajen gina halayen ɗan adam, yana cewa: “Makarantu muhalli ne na neman ilimi, fage ne na tarbiyya, kuma tushe ne na raya kyawawan ɗabi’u.”
Ya ƙara da cewa kasancewar waɗannan makarantu suna da alaƙa da Atabutul Alawiyya yana ninka alhakinsu wajen tabbatar da ilimi da kyawawan ɗabi’u a zukatan ɗalibai tare da haɓaka himma da manyan buri a cikinsu.
A bikin buɗewar, wasu jami’an gwamnati sun gabatar da jawabai, inda suka yaba da rawar Atabutul Alawiyya wajen tallafawa ɓangaren ilimi a Jahar Najaf Ashraf da inganta muhallin koyo. Wannan mataki yana cikin ƙoƙarin tarbiyyar sabuwar tsara mai ilimi da ƙwarewa, wadda kuma take da kyawawan ɗabi’u.
Murtada al-Hammami, kakakin Hukumar Ilimi ta Alawiyya, ya bayyana cewa: “Ayyukan wannan hukuma basu takaitu ga gudanar da rukunin makarantu kaɗai ba, domin hukuma ce mai cikakken tsarin ilimi da tarbiyya, wadda take aiki da nufin gina halayen ɗalibi, gano baiwarsa da kuma taka rawa wajen tsara wata makoma ta daban a fagen ilimi da tarbiyya.”









