Tawagar Atabutul Alawiyya dake Pakistan ta karrama tare da nuna godiya ga wasu fitattun mutane na addini, hukumomi da zamantakewa daga mazhabobi daban-daban, waɗanda suka taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar gudanar da shirye-shiryen “Makon Sadiqain na Ƙasa da Ƙasa”.
An gudanar da wannan shiri ne a birnin Lahore, babban birnin jahar Punjab, domin girmama haihuwar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) da jikansa, Imam Ja’far As-Sadiq (Amincin Allah ya tabbata gare shi).













