Wasu mawaƙa daga ciki da wajen Iraki, bayan kammala shirye-shiryen taro karo na biyar na Bikin Waƙoƙin Larabci na Duniya na «Babban Manzo», wanda Atabutul Alawiyya ta shirya, sun yaba da matakin fasaha da na kafafen yaɗa labarai na shirye-shiryen, tare da jinjinawa kyakkyawan tsarin shirye-shirye da ingantacciyar gudanarwa.
Haka kuma sun jaddada yanayi na musamman na al’adu da adabi da bikin ya samar a kusa da haramin Amirul Mu’uminin (Imam Ali, amincin Allah ya tabbata a gare shi), wanda ya dace da matsayin wannan munasaba.
Ahmad Kazim Khudair, wani mawaƙi daga jahar Basra, ya bayyana wa Cibiyar Labarai cewa: «Wannan biki ya haɗa kirkire-kirkire, ban mamaki da rahamar Allah; domin karanta waƙoƙin yabon Manzon Allah (amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalansa) a kusa da Amirul Mu’uminin (Imam Ali, amincin Allah ya tabbata a gare shi), yana sa mawaƙi ya ji kamar yana gaban manyan mutane biyu na duniya da Lahira. Samun damar shiga irin wannan wuri wata baiwa ce daga Allah da tayi tasiri a kan gogewata ta waƙa.»
Kyakkyawan shiri
Hassan al-Hajj Ukla, wani mawaƙi daga jahar Zi Qar, ya bayyana farin cikinsa da halartar wannan biki, inda yace: «Abin farin ciki da alfahari ne a gare mu mu kasance a wannan wuri mai tsarki da kuma a wannan lokaci mai albarka, wato ranar tunawa da haihuwar Manzon Allah (amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalansa). An tsara wannan biki a mataki mai girma ta fannoni daban-daban, abin da ya taimaka wajen nasarar shirye-shiryensa da gudanar dasu a matakin da ya dace da wannan munasaba.»
Muhammad Baqir al-Amili, wani mawaƙi daga Lebanon, shi ma ya bayyana farin cikinsa da halartar bikin, yana mai cewa: «Babban abin alfahari ne mu shiga ta ƙofar wannan birni, kuma kusa da haramin Amirul Mu’uminin (Imam Ali, amincin Allah ya tabbata a gare shi), a Sahnin Sayyada Zahra (amincin Allah ya tabbata a gare ta), mu gabatar da waƙoƙin yabo cikin soyayya, ƙauna da riƙon wilayar Manzon Allah (amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalansa).»
Ya bayyana cewa bikin ya bambanta ta fannoni da dama, daga cikin fitattun abubuwan akwai kyakkyawan shiri da shirye-shiryen da aka yi tun da wuri, wanda mawaƙan suka lura dashi tun daga lokacin da suka iso. Haka kuma ya yaba da yadda kafafen yaɗa labarai suka dau shirye-shiryen, yana mai ganin hakan ya taimaka wajen gabatar da bikin da kuma bayyana irin halartar da aka samu.
Alhakin mawaƙi
Murtada Haidari, wani mawaƙi daga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya bayyana cewa girmama wannan munasaba yana ɗora babban alhaki a kan mawaƙi dangane da ayyukan adabin da yake gabatarwa, yana mai cewa: «Na ji wannan alhaki lokacin da nake rubuta ƙasida da kuma lokacin da na halarci wannan wuri mai tsarki.»
Dokta Ahmad al-Ulayawi, wani mawaƙi daga Najaf Ashraf, shi ma ya gode tare da nuna jinjinarsa ga duk waɗanda suka taka rawa wajen nasarar gudanar da wannan biki. Ya jaddada cewa wannan taro muhimmiyar ƙari ce ta al’adu da waƙa ga yanayin adabi na birnin Najaf mai tsarki.
Yace: «Ina miƙa sahihiyar godiya da jinjinata ga Atabutul Alawiyya saboda wannan gudummawa da wannan muhimmin mataki, a ƙarƙashin sararin da ya shahara wajen renon malamai, mawaƙa da marubuta. Matakin shiri da tanadin da muka gani abu ne da ba kasafai ake samun irinsa ba a wannan fanni, domin mun ji sosai irin ingancin shiri da tsara abubuwan da aka yi.»
An gudanar da taron karo na biyar na Bikin Waƙoƙin Larabci na Duniya na «Babban Manzo» a matsayin dandali na adabi da al’adu wanda ya haɗa mawaƙa daga Iraki da wasu ƙasashen Larabawa da na Musulunci, domin girmama haihuwar Manzon Allah (amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalansa), tare da tunawa da sake nazarin sirarsa, falalolinsa da ƙimomin saƙonsa madawwami.








